Wani abu da ya janyo sabuwar takaddama shi ne rantsar da shugabannin da gwamnan jihar Darius Dickson Ishaku ya yi a kwanan nan.
Sai dai wannan mataki bai yiwa mutane da dama dadi ba ciki har da wasu daga jam’iyar ta PDP.
Amma gwamnatin jihar ta ce karancin kudi ne ya hana ta gudanar da zaben, wanda ta ce muddin har in za ta yi, za a yi watanni biyu ba a biya ma’aikata albashi ba.
Jihar ta Taraba mai yawan mutane kusan miliyan uku na karkashin mulkin jam’iyar PDP ne.
Domin jin bahasin kowane bangare dangane da takaddamar ta rashin gudanar da zaben kananan hukumomi, saurari rahoton da wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdulaziz ya aiko daga Jalingo, babban birnin jihar:
Your browser doesn’t support HTML5