Sassan sun hada da jihohin Damagaram, Maradi, da Tawa, inda makiyayan suka fara kaura da yaransu da kuma dabbobi zuwa wajen da za su samu ciyawa.
Babban daraktan ilimi, na kananan makarantu a jihar Damagaram Baru Shekarau, yace kimanin makarantu hamshin da daya ne (51) yaran makiya suka far bari domin yin kaura sanadiyar rashin abinci dabbobi.
Domin tsirar da yaran da suka yi saura hukumar abinci ta duniya, na taimakawa yaran da abinci wanda ake basu a dakunna cin abinci na makarantunsu, daraktan, makarantun Bargu Shekarau, yace akwai wadanda gwamnathin Nijar ke basu abinci akwai kuma wanda hukumar abinci ta duniya kw basu amma ba duka makarantun ke da dakunan cin abinci ba.
Ya kara da cewa a ‘yan watannin na hukumar abinci ta duniya itama tace tana famada karanci abinci kuma gashi akasarin makaratun hukumar ce ke ciyar dasu domin na gwamnatin kasar ta Nijar kadan ne.
Shugaban kungiyar Fulani makiyaya na Finan Dado Sido Amadu, yayi kira ga mahukunta da masu hanu da shuni da suyi kokari su taimakawa wannan al’amari saboda yara su samu su ci gaba da samun ilimi.
Your browser doesn’t support HTML5