Karamin Ministan Tsaron Najeriya Ya Isa Sakwato

Nigerian Defense Minister of State, Nigeria CDS Major General Christopher Musa in Sokoto

Al'ummar jihar Sakwato sunyaba da umarnin da shugaba Tinubu Yayiwa Ma'aikatar Tsaro Na Su Tare Yankin Arewa Maso Yamma Don Kawo Karshen Tsaro.

Karamin ministan tsaron Najeriya Bello Mutawalle da wasu manyan jami’an ma’aikatar tsaron Najeriya sun isa sakwato, biyo bayan umarnin shugaba Bola Ahmad Tinubu da ya bukaci manyan jami’an ma’aikatar su tare a jihar Sakwato har sai sun warware bakin zaren matsalar tsaron da ta addabi yankin.

Shugaba Tinubu ya bada wannan umarni ne, bayan mumunar kisar gillar da akayi wa mai martaba sarkin Gobir alh. Isah Bawa wanda ‘yan ta’adda masu satar mutane don neman kudin fansa suka bi shi har gida suka tafi da shi daji.

Dukkanin ministocin ma’aikatar tsaron Najeriya ‘yan yankin arewa maso yammacin Najeriya ne, kuma yankin da matsalar tsaro tayi mata katutu. Ana kyautata zaton cewa zuwan su tushen matsalar zai taimaka ya kuma karfafawa dakarun tsaro su fatataki ‘yan bindigar da suka addabi al’ummomiun yankin.