Karamar Hukumar Lafiya Jihar Nasarawa ta Dauki Matakan Tabbatar da Kwanciyar Hankali

Gwamna Tanko Al-Makura na Jihar Nassarawa

Shugaban karamar hukumar Lafiya fadar gwamnatin jihar Nasarawa Alhaji Suleiman Ahmad Wambai yace karamar hukumarsa ta dauki matakin ganin jama'a sun samu natsuwa da kwanciyar hankali.

Shugaban yayi jawabin ne domin dambarwar siyasa dake tsakanin 'yan majalisar dokokin jihar da gwamnan Alhaji Umaru Tanko Al-Makura.

Tun lokacin da 'yan majalisar suka amince a binciki gwamnan akan wasu zarge-zarge goma sha shida aka rika samun zanga zanga daga jama'a. Inji shugaban karamar hukumar Alhaji Suleiman Ahmad Wambai sun sanar da jami'an tsaro kan dambarwar dake tsakanin su 'yan majalisar da talakawa domin haka suka shawarci jami'an tsaro da su dauki matakan da suka dace.

Da yake karin haske Alhaji Suleiman yace ya kira jami'an tsaro da su kare gidajen 'yan majalisa da mutuncinsu domin akwai matsala tsakaninsu da talakawa. Akwai kuma dambarwa tsakanin gwamnan da 'yan kajalisar. Yace an yi gwamnatin PDP ta shekara 12 amma wannan gwamnati ita ce talakawa suna ganin ta damu da damuwan mutane. Sai su abokan hamayya suna ganin idan basu yi wani abu kwatanwacin haka ba bukatarsu ba zata biya ba a zaben 2015.

Suna kiran talakawa a yi zaman taimakon juna. Aikin majalisa ne tayi dokoki, ta gyara dokoki kuma ta sa ido.

Shi ma wani tsohon shugaban karamar hukuma a jihar ta Nasarawa Yakubu Muhammed yace bin doka ne kadai zai warware matsalar da ta kunno kai a jihar. Yace abubuwan dake faruwa su basu ji dadi ba. Shi gwamna ya san cewa akwai dokoki dole kuma a kalleshi a matsayin mutum dake bin dokokin. Dole kuma gwamnan ya san cewa 'yan majalisa an zabesu suyi wani aiki da ya rataya akansu. Misali, shi ne zai karbi kudi amma su ne suke da hakin su bashi izinin kashe kudin. Su sun ce ya kashe kudi ba tare da izininsu ba. Ya fito ya gayawa duniya cewa ya kashe kudin da izini. Wannan shi ne zai kawo zaman lafiya a jihar. Kada wani ya kawo fitina a jihar Kowa ya bi doka.

Idan an yi kuskure a san an yi kuskure. Amma tara jama'a su dinga zage-zage da yin tashin hankali da kone motoci ba zasu kawo zaman lafiya ba ko kai gwamnan ga nasara ba.

Ga rahoton Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Karamar Hukumar Lafiya Jihar Nasarawa ta Dauki Matakan Tabbatar da Kwanciyar Hankali - 3' 10"