Karamar hukuma a jihar Bauchi zata fara riga kafi mako-mako

Ana ba dan yaro maganin cutar shan inna

Karamar hukumar Gamawa a jihar Bauchi zata shiga aiwatar da wani tsarin rigakafi mako-mako da nufin yaki da cutar shan inna.

Karamar hukumar Gamawa a jihar Bauchi zata shiga aiwatar da wani tsarin rigakafi mako-mako da nufin yaki da cutar shan inna.

Karamar hukumar zata gudanar da shirin ne tare da tallafin wata cibiyar agaji da nufin shawo kan yaduwar kwayar cutar shan inna da ta bulla a karamar hukumar.

Jami’in gudanar da shirin na hukumar lafiya ta Duniya Emanuel Katuga wanda ya sanar da shirin ya bayyana cewa, daukar wannan matakin zai bada dama ga jami’an jinya sun isa kowanne lungu na karamar hukumar yayinda kuma za a ci gaba da aiwatar da shirin rigakafi na kasa kamar yadda aka tsara.

Ya kuma bada tabbacin cewa, za a yiwa kowanne yaro a karamar hukumar allura kasancewa za a tura jami’an aikin jinya da dama a yankin. Sabili da haka aka yi kira ga iyaye su bada hadin kai domin ganin an yiwa yaransu rigakafi.

Karamar hukumar Gamawa ce ta dauki nauyin shirin tare da hadin guiwar gwamnatin jiha da kuma Hukumar lafiya ta Duniya.