Kano Za Ta Ranto Miliyan 15 Daga Bankunan Kasuwanci

Al’ummar jihar Kano a Arewa maso Yammacin Najeriya na ci gaba da bayyana shakku dangane da yadda gwamnatin jihar zata sarrafa Naira biliyan 15 da ta ciwo bashi daga bankunan kasuwancin kasar.

Mahukuntan jihar sun ce za a yi amfani da kudaden ne wajen aiwatar da shirin gwamnati na ilimi kyauta daga matakin Firaimare suwa Sakandare.

Kimaninin makonni biyu da suka gabata ne majalisar dokokin jihar Kano ta amince da ciyo bashin, kamar yadda bangaren zartarwa na gwamnati ya bukata cikin wata wasika ga majalisar.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce babu shakka sun yi kudirin bada ilmi kyauta, kuma za su samu nasara, amma ba zai yiwu su cimma wannan burin ba da kudaden da suke samu daga Abuja, shi yasa sai sun ci wannan bashi.

Sharrudan da aka gindaya wajen ciyo wannan bashi sun nuna cewa, an rataya biyan kudaden a wuyan kananan hukumomin jihar 44 ne, la’akari da cewa dama gwamnatin zata ciyo bashin ne a madadin su.

Sai dai comrade Yahaya Shu’aibu Ungogo dake sharhin kan lamuran ilimi na cewa, ya kamata a ji ta bakin kananan hukumomin kafin a ci yo wannan bashi.

Rahotanni sunce yanzu haka ana daf da karbar wannan bashi na Naira biliya 15 tun bayan da majalisar dokoki ta bayyana goyon bayan da amincewar ta game da batun.

A saurari rahoto cikin sauti daga jihar Kano a Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Kano Zata Ranto Miliyan 15 Daga Bankunan Kasuwanci