Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya za ta kafa kwalejin horaswa da koyar da dabarun yaki da cin hanci da rashawa karkashin hukumar korafin Jama’a da hana rashawa ta jihar.
Tuni majalisar zartar wa ta Kano ta amince da kafa sabuwar kwalejin koyar da dabarun yaki da rashawar a wani mataki na samar da kwararru kuma managartan Jami’an yaki da rashawa a cewar, Barrister Muhuyi Magaji da ke zaman shugaban hukumar hana ayyukan rashawa ta jihar Kano.
“Yaranmu za su samu horon da ya kamata su samu, sannan su kansu ma’aikata za a horar da su dabarun kaucewa cin hanci da rashawa.” In ji Barrister Magaji.
Shirin na zuwa ne a dai-dai lokacin da masharhanta ke ci gaba da tsokaci dangane da dakatarwar da fadar shugaban Najeriya ta yi wa shugaban hukumar EFCC Ibrahim Mustafa Magu.
Ana dai zarginsa ne da laifukan kin yin biyayya da kuma almundahana kan wasu kudade da kadarori.
Akwai masu ra’ayin cewa, abin da ya kai ga tuhumar da ake yi wa Ibrahim Magu, ramuwar gayya ce da rashawa ke yi ga masu yakar ta.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari domin jin sharhin masanan:
Your browser doesn’t support HTML5