Kwamitin ya fara da kwato taki buhu 7000 da wasu suka karkatasu maimakon su sayarwa jama'a kamar yadda gwamnatin jihar tace a yi. Banda taki an kuma kwato kudade.
Kwamitin na bin digdigin duk wadanda suka karbi kudin taki. Dole ne kuma su dawo da kudin, inji Kwamred Muhiyi Magaji shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.
Malam Suleiman Jangefe daya daga cikin wakilan kwamitin da gwamnati ta kafa saboda sayar da takin ga manoman yankin yace sun zauna sun kasafa taki kuma sun kira wakilai biyu biyu na kowane unguwa su je su hado kudi su dauki takinsu. Wai suna cikin yin hakan shugaban mazaba ya ce masu an sayar da takin sai su gyara, wato a manta da batun takin. Suna cikin hakan magoya bayansu suka zargesu da hada baki da wasu tare da sayar da takin.
Talakawa da suka ga abun da ya faru suka kai kara.
A wani hannun kuma Muhi Magaji yace hukumarsu ta fara gudanar da bincike kan wani korafi dake zargin wasu jami'an kotun shari'a da karkatar da kudaden tara da sauran batutuwa da suka shafi kudi a kotuna ta hanyar buga rasitan bogi. Idan an karbi tara sai a buga tambari tamkar an sakawa gwamnati kudin amma ba'a saka ba.
Tuni dai lauyoyi da masu ta cewa a fannin shari'a suka fara tsokaci dangane da wannan batun. Barrister Audu Bulama Bukarti yace su kotuna su ne gatan talaka. Idan kuma kotunan basu da adalci daga karshe mutane zasu zama basu da karfin gwiwa a kotunan. Idan mutane basu da karfin gwiwa a kotu zasu fara daukar doka a hannunsu lamarin da ka kaiga lalacewa doka da oda.
Ga rahoton Ibrahim Mahmud Kwari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5