WASHINGTON D.C. —
Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi nasarar zama kungiya ta uku da ta samu damar shiga gasar gaggan kungiyoyi shida da ake yi a karshen kakar wasanni.
Kulab din Pillars ya samu gurbin buga zagaye na gaba bayan da ya yi nasara akan Delta Force da ci 3-0 a gasar Firimiya Lig ta Najeriya a wasa na 21 da suka buga jiya Litinin a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.
Fitaccen zakaran kungiyar, Rabiu Ali ne ya sa kungiyar ta Kano Pillars ta fara jin kanshin nasara da kwallon da ya ci a minti na 19 daga yankin bugun penarti.
Sauran kwallayen biyu sun fito ne daga Auwalu Ali Malam da Yusuf Maigoro, abin da ya ba kungiyar damar samun shiga gasar kungiyoyi shida.