Yau Litinin aka shiga rana ta hudu da fara aiwatar da dokar zaman gida a jihar Kano, a wani mataki na hukumomin jihar na dakile yaduwar cutar Coronavirus a tsakanin jama’a, sai dai mara sa karfi sun fara kokawa dangane da yanayin zaman.
Daukewar kafa a manya da kananan titunan Kano, baya ga kasancewar kasuwanni, kantuna da kuma cibiyoyin hada hadar jama’a a rufe, na daga cikin al’amuran da ke nuna cewa, mazauna Kano sun bi umurnin gwamnati na zama a gida.
To amma a hannu guda kuma, marasa karfi sun fara kokawa kan sabon salon yanayin damuwa da suka tsinci kansu ciki.
“Wadanda kawai suka tanada abin hannun su ne basu da matsala a wannan lokacin, hatta da burodi da ruwan sha sai ka nema ka rasa yanzu,” a cewar wani mazaunin jihar.
Sabanin ranar farko da ta biyu, inda komai ya tsaya cik a ko’ina a Kano a jiya Lahadi da maraice, akwai kalilan daga wurare da suka bude kamar gidajen man fetur, da shagunan sayar da magunguna, da gidajen burodi da sauran su.
Yanzu haka dai kungiyoyin rajin ci gaban al’uma sun fara daga muryar kiran gwamnati ta tashi tsaye domin tallafa wa talakawa tunda dai sun yi mata biyayya.
Comrade Abdulrazak Alkali shi ne Daraktan Kungiyar Organization for Community Civil Engagement.
Ya ce “taimakawa mutane yana da muhimmanci tunda dai sun yi wa gwamnati biyayya, bai kamata a kure jama’a ba har sai lokacin da suka rasa abin yi sai fitowa domin kada yunwa ta kashe su ba ."
Baya ga rashin abin kai wa bakin salati da talakawa a Kano ke fama dashi, unguwanni da dama a jihar na fuskantar karancin ruwan sha da na amfanin gida, lamarin dake kara barazana ga kiwon lafiyar al’umma.
Saurarri wannan rahoton a sauti.
Your browser doesn’t support HTML5