KANO: Hon Jibrin Isma’il Falgore Ya Zama Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Bisa Amincewar Daukacin ‘Yan Majalisar Su 40

Rantsarwar Shugabanin Majalisar Dokokin Najeriya

A jihar Kano Najeriya, Hon Jibrin Isma’il Falgore ne ya zama shugaban majalisar dokokin jihar bisa amincewar daukacin ‘yan majalisar su 40. A wani kwarya-kwaryar biki na kaddamar da majalisar ta 10, sabon shugaban ya yi alkawarin tafiya tare da dukkanin ‘yan majalisar domin ciyar da jihar gaba.

Akawun majalisar dokokin ta Kano ne Alhaji Ali Maje yake rantsar da sabon shugaban majalisar wanda daga bisani ya ci gaba da jagorantar zaman majalisar na farko a yau Talata 13 ga wannan wata na Yuni, 2023.

Gabanin haka sai da sabon shugaban majalisar dokokin ta KANO ya bayyana aniyarsa ta biyayya da gwamnati da kuma tafiya tare da dukkannin mambobin majalisar ba tare da nuna wariya ba, kamar yadda yake kunshe a cikin lafuzzan sa na rantsuwa.

Rantsarwar Shugabanin Majalisar Dokokin Najeriya

Bayan kammala zaman sabon shugaban majalisar dokokin ta Kano Hon Jibrin Isma’il Falgore ya yi wa Muryar Amurka karin bayani game da kudirorinsa da kuma sigar da zai bi wajen jagorantar majalisar, inda ya nanata biyayya ga manufofi da tsare tsaren gwamnatin Jam’iyyaru ta NNPP. Sai dai ya ce a tsarin shugabancin sa, kofar sa a bude take ga dukkannin ‘yayan majalisar domin tabbatar da shugabanci na gari.

Hon Abdul A. Abdulhamid, wanda ya yi wa majalisar kome bayan hutun shekaru takwas ya kawar da hasashen wasu cewa, la’akari da yadda aka gudanar da zaben shugabancin majalisar akwai yuwuwar majalisar Kanon ta goma ta zama kara zama ‘yar amshin shata.

Jam’iyyar NNPP mai gwamnati a Kano nada jimlar mambobi 26 a zauren majalisar yayin da APC mai hamayya keda 14, amma Hon Garba Yau Gwarma daga mazabar Gari da Tsanyawa yace yawan ‘yayan NNPP a zauren ba zai ba su damar yin cinye ba a dukkanin al’amura, domin kuwa suna bukatar juna.

Sauran wadanda aka zaba sun hada da Hon Muhammad Bello Butu-Butu a matsayin mataimakin shugaban majalisar da Hon Lawan Hussaini shugaban masu rinjaye da Hon Labaran Abdul Madari shugaban marasa rinjaye sai Hon Ayuba Labaran Durum a matsayin mataimakinsa.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

KANO: Hon Jibrin Isma’il Fagore Ya Zama Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Bisa Amincewar Daukacin ‘Yan Majalisar Su 40