Wakilan kungiyoyi masu zaman kan su dake aikace aikacen tabbatar da zaman lafiya da takwarorin su dake ayyukan kare hakin bani adama a matakin Najeriya da sassan Afrika ne suka halarci taro wadda ya wakana a nan Kano.
Kazalika, wakilai daga sassan duniya da kuma ofisoshin diplomasiyya na wasu kasashe sun bada gudunmawa ga zauren taron ta kafar sadarwa ta internet wato ZOOM
Rawar da hukumomi da kungiyoyi da cibiyoyin gwamnati da-ma daidaikun mutane ka iya takawa wajen wanzar da adalci da kare hakkin dan adam a kowane lokaci da nufin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umomi sune batutuwan da suka mamaye ajandar taron.
Ku Duba Wannan Ma Kungiyoyin Kare Hakkokin Mata Sun Bukaci A Dauki Matakan Yaki Da Auran Wuri Don Kara Ba Mata Damar IlimiProf Buhari Isa shine babban Jami’in gudanarwa a ofishin kula da kungiyoyin diplomasiyya dana kare hakkin dan adam na Afrika, ya fayyace ayyukan da suka sanya a gaba domin cimma manufa. Ya ce suna ayyukan zamna lafiya da kare hakkin dan Adam da shirya zama na bita akan mahimmancin adalci da kuma kyautatawa.
A yayin taron wadda wakilai daga kasashen Turai da nahiyar Asiya suka bada gudunmawa ta kafar Zoom, kungiyoyin kare ‘yancin bil’adama dana diplomasiyya da zaman lafiya hadin gwiwa da School of LEADERSHIP ta Amurka sun karrama Hajiya Hassan Saminu Turaki da lambar ambassadon zaman lafiya bisa la’akari da kokarinta ta wannan fuska.
Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da hukumar kare hakkin bil’adama ta Najeriya ke cewa kunci da tsadar rayuwa a kasar na kara alkaluman cin zarafi da take hakkin bil’adama a tsakanin iyalai.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5