Kannywood na fuskantar barazana daga masu satar fasaha sakamakon bin matakin karshe na harkar kasuwancin fina-finai da masu shirya fina-finan da masana’antar Kannywood suka dauka inji mai shiryawa Umar Sani Kofar Mazugal wanda aka fi sani da Umar UK.
Umar ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir inda ya ce a kasashen da aka cigaba masu harkar fim na fitar da fina-finan su ta hanyar bin matakan tallatawa da sayar da fina-finansu ta hanyar fitar da su a silma, sa’annan mataki na biyu a gidajen talabijin kafin ya fita ga jama’a.
Ya ce yin hakan na dakile masu satar fasaha samun damar sata har sai mai fim ya maida ribarsa, yana mai cewa, wadanda suka fara harkar fim yawanci shi’awa ce ta ja su, ba tare da sunyi la’akari da gudanar da bincike ba kafin a tsunduma ga harkar.
Umar ya ce matakan da kasashen waje ke bi sune ta amfani da gidajen kallo na silma, sannan gidajen talabijin inda ake basu hakkin su kamar yadda ya kamata, dan haka babu yadda za’ayi mai satar fasaha ya sata, sa’annan daga karshe bayan anbi wadannan matakai ne fim zai fita kasuwa.
Your browser doesn’t support HTML5