Hukumomin kasar dai sun dora alhakin karancin man fetur din ne a kan lamarin gurbataccen man da ya kai kimanin lita miliyan 170 da aka shigo da su daga Turai a watan Janairu. A watan Fabrairu, gwamnati ta ba da sanarwar cewa ta fitar da lita biliyan daya na man fetur daga asusun ajiyar kasar don daidaita rarrabawa.
Sai dai a yayin da ake samun hauhawar farashin mai da iskar gas a duniya, lamarin dai na ta tafiyar hawainiya kuma yana shafar tattalin arzikin kasa baki daya. A wannan makon, Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta ce hauhawar farashin kayayyaki a kasar ya karu zuwa kashi 15.7 a shekara.
"Lamarin na neman ya zame ruwan dare," in ji wani mazaunin Abuja kuma direba mai suna, Mohammed Enesi.
Najeriya ita ce kasa mafi arzikin man fetur a Afirka, amma tana kan fama da biyan bukatunta na makamashi.
Kimanin kashi 47 cikin 100 ne na ‘yan Najeriya ke samun wutar lantarki idan har akwai, kamar yadda kiyasin bankin duniya ya nuna. Hukumomin Najeriya a shekarar 2020 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar wutar lantarki da takwarorin aikinsu na Jamus domin inganta samar da wutar lantarki.
Sai dai masana sun ce karancin makamashi na illa ga 'yan kasar.
"Har yanzu ba mu sami damar daidaita yanayin ba," in ji manazarci Rotimi Olawale. “A gaskiya a cikin shekaru biyun da suka gabata ba mu ga irin wannan karancin man fetur da muke gani a yanzu ba.
A cikin makon nan ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa 'yan kasar alkawari cewa nan ba da jimawa ba za a kawo karshen matsalar man fetur da wutar lantarki.
Amma har sai lamarin ya daidaita, miliyoyin mutane da kasuwanni za su ci gaba da shan wahala.