Kananan Manoma Na Bukatar Tallafin Kayan Aiki

  • Ibrahim Garba

Kayakin noma

Kananan manoma sun ce muddun aka tallafa masu da kayan noma na zamani, za su habbaka bangaren noma


Kananan manoma na ganin za su iya habbaka noma muddun aka tallafa masu da hanyoyin noma na zamani saboda su shawo kan kalubalen da su ke fuskanta. Daya daga cikinsu ya ce hanya guda ita ce a samar da motocin noma wadanda za su taimaka tun daga haru har zuwa huda idan sun girbe kayan gonakinsu kuma sai su biya.

Kuma ya kamata gwamnati ta rinka saye da daraja ta yadda zai taimaki manoman. Ya ba da misali cewa idan jama’a na saye kan Naira 100 sai ita kuma gwamnati ta saya akan Naira 120 don ta karfafa masu gwiwa. Kuma a rinka cire kudin da ya kamata manoman su biya ta wannan hanyar.

Ya ce hatta taki wani manomin bai da Naira 1000 na saye. Don haka saidai a rinka ba su bashi da nufin su rinka biya ta wannan hanyar wato ta wajen cire kudin bayan an yi girbi. Kuma ya kamata a rinka rage kudin takin shima.

Your browser doesn’t support HTML5

Kananan Manoma