Kananan hukumomi 200 suna fuskantar barazanar yaduwar cutar polio,

Ana ba wani dan yaro maganin cutar shan inna

Babban jami’ain kiwon lafiya na jihar Bauchi yace kananan hukumomi maitan daga cikin 774 na Najeriya suna fuskantar cutar polio

Babban jami’ain kiwon lafiya na jihar Bauchi yace kananan hukumomi maitan daga cikin 774 na Najeriya na cikin hadarin barkewar cutar shan inna.

Sakataren cibiyar Nisser Umar ya bayyana haka ne yayin kaddamar da aikin rigakafin shan inna da kari da aka gudanar a jihar a Karamar hukumar Ganjuwa,

Bisa ga cewarshi, kananan hukumomi 15 daga cikin ishirin na jihar na daga cikin kananan hukumomin dake cikin hadarin barkewar cutar. Sakamakon gaza yiwa kananan yara da dama rigakafi da kuma kaurar da tafiyar al’umma daga jiha zuwa jiha.

Mr. Umar ya yi kira ga iyaye su tabbata an yiwa ya’yansu rigakafi, yayinda ya bayyana cewa, an kara yawan ma’aikatan da zasu gudanar da aikin rigakafin. Bisa ga cewarshi, gwamnati jiha tare da hadin guiwar kananan hukumomi ta sayi magani da za a iya yiwa yara miliyan daya da dubu dari tara rigakafi.

Za a dauki kwana hudu ana gudanar da aikin rigakafin.