Zargin da kamfanonin suka yi yana zuwa ne a daidai lokacin da shi babban bankin ya dage cewa yana bin ka’idojin da suka dace wajen bada rance tare da tallafawa kamfanonin cikin gida da kudaden kasashen waje domin su cigaba da gudanar da harkokinsu.
A taron da kamfanonin suka yi a Lagos, sun zargi babban bankin da gazawa da kuma yin zagon kasa ga tsarin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na inganta harakokin kasuwanci tare da samar da aiki wa dimbin matasan kasar.
Shugabannin taron sun yi kira ga gwamnati ta taimaka masu kai tsaye domin su cigaba da ayyukansu, musamman, kamar yadda suka ce, kamfanonin basa samun kudaden waje daga babban banki.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5