Kamfanin Toyota ya gabatar da ingantaccen mutum-mutumi na Robot mai suna “T-HR3” da ya kirkiro. Wanda aka inganta shi da wasu abubuwa, ta yadda zai yi iya aiki kusan babu banbanci da yadda mutane ke gudanar da rayuwarsu ta yau da kullun.
Robot din dai za a dinga sarrafa shi ne daga waje daya, amma shi kuwa yana ko ina a fadin duniya, don gabatar da aikin da duk ake so ya yi. A duk lokacin da ake so ya yi wani abu, kawai mutun zai iya motsa jikin shi da niyyar yin wani abu, sai mutummutumin ya yi abun da aka umurce shi ya yi.
Hasali ma, ana ganin bada jimawa ba likitoci za su fara amfani da shi, wajen aikin tiyata ga marasa lafiya a ko'ina a duniya, ba tare da likita na wajen ba.
Haka mutane da ke bukatar halartar wani taro amma kuma suna da wasu hidindimu ba za su samu dammar halarta ba, suna iya sa robot din ya wakilce su, kuma su gabatar da duk wani abu da suke bukatar gabatarwa kamar suna wajen.