A jiya Litinin, kamfanin fasahar SpaceX ya bada sanarwar harba kumbon wasu na'urorin tauraron dan’adam guda 60, wannan shine karo na biyu da kamfanin ya tura irin wadannan na'urorin da zasu taimaka wajen samar da ingantacciyar hanyar yanar gizo a ko'ina a duniya.
Da safiyar jiya ne kumbon dake dauke da na'urorin ya tashi zuwa sararin samaniya. Farantan na'urorin tauraron dan adam din, masu nauyin kilogram 260 kowannensu, zasu hadu da wasu guda 60 da aka harba a watan Mayun da ya gabata.
Mai kamfani kuma shugaban SpaceX Elon Musk, naso ya harba dubban wadannan na'urorin ta yadda zasu dinga zagayawa, don su samar da hanyar yanar gizo mai matukar gudu a ko'ina. Yana kuma shirin ganin sun fara aiki a shekara mai zuwa a arewacin Amurka da kuma Canada, bayan haka zasu yi aiki a wuraren dake da jama'a a duniya bayan kamfanin ya harba na'urorin sau 24.
Wannan ne kuma karon farko da kamfanin SpaceX ya sake yin amfani da goshin kumbon da ya taba harbawa. Kamfanin wanda ke jihar California, ya kan sake amfani da wasu sassan kumbon da yayi amfani da su a baya don rage kashe kudi.