Hukumar kula da shirya gasar Lig a Najeriya, tace ta dage takunkumin da ta kakabawa dan wasa Rabi'u Ali, ta kara da cewar dagewar ta fara aiki ne tun daga ranar 25 ga watan Nuwambar 2019, a cewar jami’in watsa labarai na Kano Pillars Rulwanu Idris Malikawa.
A wata sanarwa dauke da sa hannun babban jami’in gudanarwa na LMC, Malam Salihu Abubakar a ranar Litinin da ta gabata, ya ce kamfanin ya dage hukuncin ne sakamakon rubutacciyar wasika da suka samu daga dan wasan Rabiu Ali da kungiyar Kano Pillars FC, tare da kungiyoyin al’umma na bada hakuri game da laifin da yayi, da kuma nuna nadamarsa game da abun da ya faru yayin gasar cin kofin Super Super na shekarar 2019.
Yanzu haka Rabiu Ali zai samu damar fafatawa da Plateau Utd a wasan mako na shida ranar Lahadi 1 ga Disambar 2019 cikin gasar NPFL na bana.
Sai dai LMC ta gargade shi da ya kasance jakada na gari ga Kano Pillars FC, kamfanin LMC, hukumar kwallon kafa ta Najeriya da kuma al'ummar da ya tsinci kansa.
Ana ta bangaren kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, a karkashin jagorancin Alhaji Surajo Shu'aibu Yahaya, tare da dan wasan Rabi'u Ali sun bayyana godiyar su ga kamfanin na LMC wanda ke shirya gasar Lig a Najeriya, bisa amsa rokon su da su kayi.
Suna kuma bada tabbacin cewar kungiyar da kuma 'yan wasanta zasu ci gaba da bin doka da oda a kowane lokaci.
Dan wasan ya bukaci magoya bayan Kano Pillars da su kwantar da hankulansu domin martabar kulob din zai dawo, tunda yanzu kungiyar tayi wasa biyar ba tare da tayi nasara ba.
Idan za'a tuna LMC ta dakatar da Rabiu Ali wasanni 12 ne sakamon cin zarafin Alkalin wasa da yayi yayin gasar Super Cup ta 2018/2019 da su kayi tsakaninsu da Enugu Rangers a birnin Ikko.