Kamfanin Samsung Ya Dakatarda Sarafa Wayar dake Kama Wuta

Samsung logo

Kamfanin kayan lantarkin Samsung na kasar Koriya ta Kudu ya sanar da cewa ba zai cigaba da sarrafa wayar hannun “komai da ruwanka ta Galaxy Note 7” ba biyo bayan rahotannin da suka bazu a fadin duniya akan irin yadda wayar ke daukar zafi fiye da kima.

Kamfanin ya sanar yau Talata cewa zai dakatar da sarrafa wayar baki daya ne don kiyaye lafiyar masu amfani da ita.

Tunda farko a yau kamfanin na Samsung ya bada sanar cewa ya dakatar da sayar da wayar Galaxy Note 7, ko musayar ta a fadin duniya, ya kuma yi kira ga masu amfani da ita da su daina ba tare da bata lokaci ba. Kamfanin na kasar Koriya ta kudu ya yi hasara kashi 8 cikin dari a hannayen jarinsa yau Talata.

Dama kusan wata guda ke nan ba wayar ta Note 7 a kasuwa sosai tun lokacin da kamfanin ya sanar da maido da wayoyi miliyan 2.5 saboda matsalar batiri a farkon watan Satumba. Kamfanin kuma ya ba duk masu yin amfani da wayar damar yin musaya, kafin sabbin rahotanni suka nuna cewa ko sabbin suna mugun zafin, abinda ya kawo shakka akan irin kulawar da kamfanin yake kan ingancin kere-kerensa.