Kamfanin Philips ya dukufa wajen kula da lafiyar mata da kananan yara

A Laotian soldier covers the body of a plane crash victim with a sheet on the bank of the Mekong River in Pakse, Laos, Oct. 18, 2013.

Kamfanin kiwon lafiya a Afirka Philips Healhcare ya kaddamar da wani shirin kula da mata masu juna biyu da jarirai a Najeriya

Kamfanin kiwon lafiya a Afirka Philips Healhcare ya kaddamar da wani shirin kula da mata masu juna biyu da jarirai a Najeriya.

Kamfanin ya dauki wannan matakin ne a yunkurinshi na inganta kula da mata masu juna biyu da kananan yara a Najeriya da kuma fadada ayyukan jinya. Kamfanin Philips Healthcare Africa ya samar da sababbin na’urorin aikin jinya tare da daukar wani ma’aikaci a matsayin manaja da zai yi aiki a Najeriya.

Matakan da Kamfanin Philips ya dauka na cimma wannan burin sun hada da samar da kayan aiki da horaswa ga ma’aikatan jinya a matakai dabam dabam kan kula da mata masu juna biyu da nufin ganin sun haihu lafiya da kuma tabbatar da lafiyar jarirai.

Kamfanin ya kuma hada hannu da ma’aikatar lafiya ta kasa inda yake samar da kayan aiki na zamani da suka hada da na’urar daukar hoton tantance kwayar cuta da na’urar gano sankaran mama na mata.

Banda Najeriya, kamfanin Philips ya kaddamar da wannan shirin a kasashe hudu da nufin ganin an cimma burin muradun karni da shawo kan mace macen mata da kananan yara kafin shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.