Kamfanin NNPC Ya Cimma Yarjejeniya Da Manyan Abokan Hulda, Wanda Hakan Ya Kawo Karshen Dinbin Asarar Da Najeriya Ke Yi

Hedikwatar NNPC

A wani mataki da ya kawo karshen wata dadaddiyar takaddama tsakain kamfanin man Najeriya NNPC da abokan huldarsa, bangarorin biyu sun cimma jiyuwa, wanda hakan ya kawo karshen tafka asara da Najeriya ke yi.

Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC da manyan kamfanoni da ya ke hulda su sun cimma wata yarjejeniya wacce ta kawo karshen dadaddiyar takaddamar da ke tsakanin bangarorin biyu, lamarin da ya kusan janyo asarar dala biliyan 9 ga kasar, a yanzu haka dai sun rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya, wadda za ta ba da damar tono mai daga karkashin ruwa da adadinsa ya kai gangan har biliyan goma a dunkule. Hakan na cikin tanadin sabuwar dokar a sashi na 311 na masana’antar man fetur a kasar

Wannan ci gaban da aka samu dai ya biyo bayan umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya bukaci a shawo kan duk wasu rikice- rikice da ke haifar da rashin jituwa da saukin kasuwanci tsakanin kamfanonin mai na kasa da kasa da Najeriya.

shugaban Kamfanin Man Fetur na NNPC Malam Mele Kolo Kyari ya fadi cewa wannan mataki da aka dauka zai samar da sabin kudaden shiga da yanayin mai kyau kana mataki ne da zai bunkasa fannin danyen mai a Najeriya da kuma hanya ga masu zuba hannayen jari

Malam Mele Kyari

Shugaban bangaren kamfanin NNPC da ke sa ido kan jari da gwamnati ke da shi a fannin albarkatun mai a Najeriya, Bala Wunti, ya bayyana cewa a yanzu haka akwai hadin gwiwa tsakanin abokan huldar kamfanin wajen aikin tono mai da a baya a ka yi watsi da su. Kuma tuni ake sa ran samun dala biliyan hudu daga kwangilar ta wannan shekara.

Yarjejeniyar NNPC da Abokan Hulda

Kazalika kamfanin NNPC ya kaddamar da wata manhaja da za ta sa ido tare da bai wa 'yan kasar damar ba da bayani ga kamfanin kan duk wani da ake zargi da satar man fetur ko barnata bututun mai a yankunan da ke kewaye da mai a Kasar kamar yanda shugaban kamfanin Malam Mele Kyari ya bayyana.

Yarjejeniyar NNPC da Abokan Hulda

Duk wannan dai na daga cikin shirin da gwamnatin tarrayyar Najeriya ta bullo da su da za su taimaka wajen shawo kan kalubalen samar da kudade a bangaren man fetur da iskar gas da kuma habbaka arzikin man fetur na kasar da inganta tattalin arziki, kuma ana sa ran wannan cigaban zai bude hanyoyi ga kasar wajen samun dala biliyan 500 na kudaden shigarta.

Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim:

Your browser doesn’t support HTML5

NNPC da Abokan Hulda.mp3