Kamfanin Google Zai Kaddamar Da Wasan Bidiyo Game

A jiya Talata kamfanin Google ya bada sanarwar cewar zai fadada damar buga wasan bidiyo game a farfajiyarsa da ake kira ‘Stadia’

Shirin zai ba da damar saka nau’uka na bidiyo games a duniyar giragizai, wanda zai shiga cikin na’urori kamar su waya da kwamfuta a duk lokacin da mutun ya bukaci hakan.

Duk dai da cewar ba sanar da ko nawa kudin siyan game din zai kasance ba, kuma ba a sanar da wadannen nau’ukan wasannin za’a samu a kafarba, amma dai kamfanin ya bada tabbacin cewar za’a fara amfani da kafar daga nan zuwa karshen shekara mai zuwa 2019.

​Kamfanin ya sanar da hakan ne a lokacin wani taro na masana wasan bidiyo game da aka gudanar a nan kasar Amurka, da zummar kawo sauki ko kirkiro wasu sababbin hanyoyin amfani da bidiyo game din.