A wani rahoto da gidan jaridar USA TODAY ya rawaito yace kamfanin google mai shafin bincike kan yanar gizo, na kokarin fito da wani sabon shafinsa na yanar gizo wanda zai maida hankali kan yara ‘yan shekara goma sha biyu zuwa kasa.
Abinda ya janyo hankalin ma’aikatan kamafanin fasahar na google shine kowa na haifar yara, kuma yaran na amfani da ire iren wadannan shafuka wajen bincike a wannan zamani namu. Domin kiyaye yaran wajen binciken abubuwan da basa bukatar koya ko gani.
Shugaba mai kula da bangaren aikin injiniya na kamfanin google Pavni Diwanji ya fadawa gidan jaridar USA TODAY, “muna tsammanin kawo wannan fasahar ta zama abin kace nace, amma gaskiyar lamari shine yaran yanzu nada wannan fasahar ta bincike akan yanar gizo a gidajensu harma da makarantu.”
Wannan hanyace dai ta taimakawa iyaye yara wajen ganin suna kula da abubuwan da ‘ya’yansu ke bincika da kuma dubawa kan shafin yanar gizo.
Your browser doesn’t support HTML5