Kamfanin Facebook ya soke izinin shiga shafin na wadansu mutane 51 da shafukan wasu kamfanoni 36 da kuma na wasu kungiyoyi 7, bayan da kamfanin FireEye mai samar da tsaro a yanar gizo ya gano dukkansu na boge ne kuma an kirkiresu ne daga kasar Iran.
Haka kuma an rufe wasu shafukan kafar sadarwa ta Instagram.
Jiya Talata kamfanin FireEye ya fitar da rahotan cewa shafukan na bogi an shirya su yadda zasu yi kamar daga Amurka aka kirkiresu, kuma shafukan yada labarun gabas ta tsakiya ne, domin su rinka yada farfagandar Iran.
Labaran da ake kafewa akan shafukan sun hada da wadanda ake yi cikin harshen Turanci da Larabci, ciki har da tattaunawa akan siyasar Amurka da Birtaniya.
Wani labari da suka kafe na cewa hanyar da ta fi dacewa a girmama ‘dan jaridar nan na Saudiyya da aka kashe Jamal Khashoggi, itace Amurka ta dakatar da aika agaji ga rundunar da Saudi ke jagoranta a fada da ‘yan awaren Yamal da Iran ke marawa baya.