WASHINGTON D.C. —
Kamfani shafin sada zumuncin Facebook ya sanar da cewa yana hana yabo, goyon baya, da kuma wakiltar turawa masu kyamar wadanda ba turawa ba a shafikan sa da kuma na Instagram, wanda ya mallaka.
Kamfanin ya sanar da haka jiya Laraba a shafin yanar gizo, yana mai cewa, "a bayyane yake wadannan ra'ayoyin suna da nasaba sosai da kungiyoyin kiyayya, kuma ba su da wani wuri a shafukan mu."
Sanarwar ta Facebook ta ce, kamfanin ya dade da hana maganganun tsana da ba'a, da kuma nuna kabilanci, ko banbancin addini. Ko da yake, shafin Facebook na ba taruwa masu ra'ayin kishin kasa izinin bayyana ra'ayoyin su domin sun banbanta da masu ra'ayin wariyar launin fata.