Kamfanin Facebook Na Cigaba Da Karfafa Matakan Tsaronsa

Tun bayan wani babban kutse da akayi ma jama’a a shafukansu na Facebook, kamfanin ya fito da wasu sababbin hanyoyin kare shafin yanar sada zumuncin. Kutsen da aka yi ya shafi sama da mutane milliyan 50 a duk fadin duniya.

Kamfanin ya shawarci jama’a da su kokarta wajen sabunta harrufa ko lamba, ko kalmar bude shafin su ta sirri da ake kira password da turanci akai-akai, don kaucewa shiga tarkon ‘yan kutse.

Kamfanin ya kuma karfafa matakan tsaron shi, inda a duk lokacin da mutun ya bukaci sabunta bayanansa, na’urar zata rike bayanan, da kuma kokarin ganin duk wani bayani da aka shigar da bai yi dai-dai ba tsarin ba zai ki amincewa da shi.

Kamfanin ya kara da cewar akwai bukatar mutane su dinga amfani da wasu bayanai, da babu wanda zai iya sanin su wajen amsa tambayoyin sirrinsu, kuma kada mutane su dinga amfani da shekarun haihuwar su da na ‘ya’yansu, ko na mata da masoyansu. Haka zalika kada mutane su dinga amfani da sunan gari, kasa da dai wasu sunaye masu nasaba da mutun.

Haka nan kamfanin ya ja hankalin mutane wajen saka password din su a na'urar kwanfutar kasuwa, ba tare da duba alamar nan dake ce ma mutun ya ajiye password dinsa na din-din-din ba, don ta haka ake sace bayanan mutun.

Kamfanin ya dau alwashin kawo karshen satar bayanai ga ‘yan kutse, kana da kawo karshen labaran kanzon kurege da akan yada ta kafar shi.