‘Yan arewa da Masu fafutikar kare hakkokin bil’adama a Najeriya sun dora laifin tururuwar da matasan arewa Majiya karfi ke yi zuwa Kudu maso yammacin Najeriya domin “Ci Rani” akan shugabannin Arewa marasa hangen nesa. Wannan zargi na zuwa ne bayan kama wasu matasa ‘yan arewacin kasar da aka yi a karshen makon jiya su 123 bayan shigowar su birnin Legas.
Koda yake, tuni rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta saki matasan ‘yan asalin jihar Jigawa da tun farko aka kama bisa zargin cewar watakila masu mugun nufi ne suka shiga birnin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas DSP Bala Elkana, yace lallai an kama matasan kuma kwamishinan ‘yan sanda bai bata lokaci ba ya tura jami’an ‘yan sanda domin su gudanar da bincike. Bayan binciken sun gane matasan ba su da wani mugun nufi akan al’ummar jihar, sun zo ci rani ne kawai, a cewar DSP Elkana.
Alhaji Ado Dansudu, shugaban kungiyar ‘yan arewa a Legas, ya bukaci a kama wadanda suka gabatar da wannan zargin ya kuma dora laifin akan wasu shugabannin arewa da basa tallafawa ‘yan yankin su.
Su ma masu kare hakkokin bil’adama irin su Musa Jika na kungiyar Amnesty international ya ce irin wannan kamen da aka yi cin zarafi ne na bil’adama wanda bai kamata hukumomi su zura ido su na kallo ba. Ya kuma yi kira ga shugabannin arewa akan su tashi tsaye wajen samar da aiki da tsaro ga al’ummarsu domin hana su zuwa ci rani.
Ga karin bayani cikin sauti daga Babangida Jibrin.
Your browser doesn’t support HTML5