Yarinyar ta dauki aniyar tayar da bamabamai a cikin al'umma ne a garin Waza cikin karamar hukumar Kwalkwata kusa da kan iyaka da kasar tarayyar Najeriya.
Kafin ta kai inda ta shirya kai harin jami'an tsaro da 'yan banga sun dagota suka fafareta nan take kuma ta tayar da bam din dake jikinta ta tarwatsa kanta. Ita kadai ce ta rasa ranta.
Harin ya zo daidai ne lokacin da shugaban kasar Paul Biya yake jawabin na sallamar tsohuwar shekara da kuma yin lale marhaban da sabuwar shekarar 2016. A jawabin ya yabawa dakarun kasar da 'yan aikin sa kai da 'yan banga na nuna kishin kasarsu domin tare wasu bata gari.
Alhaji Sani masani akan harkokin tsaron kasar Kamaru yace gudummawar da Amurka ta kawo ake zaton zai taimaka ainun wajen yaki da 'yan ta'ada saboda sojojin Kamaru basu kware ba wajen yaki 'yan ta'ada kaman 'yan Boko Haram. Yace dole ne a yi anfani da fararen hula da zasu shiga cikin 'yan ta'adan domin a shwao kansu.
Shi ma gwamnan jihar arewa mai nisa Malam Mijinyawa ya yabawa dakarun tsaro da 'yan sa kai da 'yan kato da gora wajen jajircewa da suka yi akan kare kasarsu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5