Kauyen Kalagari na kusa da garin Kwalbata inda 'yan matan suka yi kokarin kutsawa cikin masallaci kafin 'yan kato da gora su tunkaresu daga bisani suka kwance damarar jikinsu suka tada bamabamai.
Bamabaman sun yi sanadiyar mutuwar mutane hudu na take da suka hada da jami'an tsaro guda biyu.Su ma 'yan kunar bakin waken sun sheka lahira tare da jikata mutane da dama. Yanzu dai ana kulawa da wadanda suka jikata a asibitin garin Kwalbata.
Wannan harin bayan nan ya daurewa jama'a kai saboda ikirarin da dakarun tsaron kasar keyi na samun galaba kan maharan Boko Haram.
Wani Malam Bukar dan garin Kalgari ya fadawa Muryar Amurka cewa lamarin ya fi karfinsu. Yace jama'arsu sun mutu kuma basu da komi ko aikin yi. Ya kira gwamnati da ta shigo ta kawo masu dokin gaggawa. Yace sun gaji kuma idan ba'a yi hankali zasu gudu. Kodayake shugaban kasar yace suna yaki da 'yan Boko Haram yace su basu gani a kasa ba maimakon hakan ma sun shigo zasu kashesu.
Ga karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5