Shugaban Kamaru Paul Biya ya ce ya yi nasarar fatattakar 'yan Boko Haram daga cikin kasar, don haka da matukar bukatar sake zabensa a zaben Shugaban kasar na ranar 7 ga watan Oktoba, saboda ya sake farfado da abubuwan da su ka durkushe.
WASHINGTON D.C. —
Biya na magana ne a garin Marwa, a daya daga cikin 'yan ziyarce-ziyarcen da ya kan fice daga Fadarsa ya yi, wanda ba kasafai ya kan yi ba, don kaddamar da yakin neman zabensa.
Mata sun yi sutura da tufafi masu launukan jam'iyyar CPDM ta su Paul Biya a ranar Asabar, su ka marabce shi a garin na Marwa. Sun yi ta bai wa Biya tabbacin cewa za su kada masa kuri'a, don ya sake shugabantar Kamaru na wani sabon wa'adi na tsawon shekaru 7, wanda zai fara aiki daga ranar 7 ga watan Oktoba.
Jam'iyyar CPDM ta kwaso mutane sama da 30,000 daga sassa dabam-dabam na arewacin Kamaru zuwa garin Marwa. An kafa hotunan yakin neman zaben Biya a ko ina a garin na Marwa.