Kotun kasar Kamaru ta yiwa wasu mutane su dari da tara da ake zargin suna da hannu a kungiyar Boko Haram hukuncin daurin rai da rai
Kotun da ta yanke hukumcin ta ti zamanta ne a jihar arewa mai nisa, jihar dake makwaftaka da yankin Najeriya maifar kungiyar Boko Haram.
Hukumcin ya jawo kace-nace a tsakanin al'umma musamman masana harkokin shari'a.
Barrister Umaru Mala yace a matsayinsa na lauya shari'ar bata dace ba saboda an taka doka saboda kowanensu bai samu lauya da zai kareshi ba.
Shi ma Malam Bala Ayuba dan rajin kare hakkin bil Adama yace basu ji dadin hukumcin ba saboda daga cikinsu akwai wadanda basu san hawa ba bale sauka. Da kamata yayi gwamnatin tayi binciken kwakwaf kafin ta yanke hukumci.
Ga rahoton Garba Awal da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5