Kamaru ta Rufe Kan Iyakokinta da Najeriya

Kan Iyakan Najeriya.

Kan Iyakan Najeriya.

Kayayyaki har sun fara hau-hawa a Kamaru sanadiyar rufe kan iyakoki.

Gwamnatin kasar Kamaru ta rufe kan iyakokinta da Najeriya, domin tsoron yaduwar cutar Ebola, wanda ya bulla a Najeriya.

Wani Malami kuma dan kasuwa mazaunin Garwa, a kasar Kamaru, Ibrahim Sanda, yace daukan wannan mataki ya biyo bayan taron da akayi ne da Ministan kiwon lafiya na Kamaru ne kan matakan hana cutar shiga kasar ta Kamaru.

Ya kara da cewa rufe kan iyakokin da Kamaru tayi ba karamar illa za yiwa kasar ba domin a cewar sa kayayyaki har sun fara hau-hawa.

A kwai cinikayya tsakanin Kasar ta Kamaru da Najeriya ta fanoni daban-daban kamar Kayayyaki abinci zuwa man fetur.

Your browser doesn’t support HTML5

Kamaru ta Rufe Kan Iyakokinta da Najeriya - '431"