Wani harin kwantar bauna da wasu da ba'a san ko su wanene ba suka kai kan wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya akan iyakar Kamaru da Najeriya ya rutsa da mutane biyar.
Tawagar ta kunshi wadanda suka samu kwangilar shata iyakokin kasashen biyu kuma aikin ne ya kaisu Najeriya daga inda suka tsallaka suka shiga kasar Kamaru kafin biyar cikinsu su gamu da ajalinsu.
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya ko MDD na kasashen Afirka Ta Yamma Muhammad Ibn Chambers yayi Allah wadai da harin.
Kazalika kasar Kamaru tace ba zata bari a yi mata irin wannan aika-aika ba akan iyakokin kasarta. Gwamnati ta sha alwashin daukan duk matakan da suka dace domin zakulo wadanda suka aikata danyen aikin.
Mr. Nasiru Muhammad wakilin ministan harkokin cikin gidan Kamaru yace shugaban kasa ya tabosu yace lallai lallai a cigaba da bincike har sai an gano mutanen. Yace tunda aka tabo Majalisar Dinkin Duniya an tabo duniya gaba daya ke nan.
Nasiru Muhammad yace yanzu dai suna zargin 'yan ta'adan Boko Haram. Akwai kuma wasu 'yanbindiga da suke zarginsu da hannu a kisan kodayake basu da tabbas. Har yanzu suna kan bincike.
Garin Koncha inda lamarin ya faru, inji Nasiru bangare ne da kungiyar Boko Haram take yawan kai hare-hare shi ya sa suke kyautata zaton 'yan Boko Haram ne.
Nan da sati daya gwamnatin Kamaru tayi alkawarin warware wannan matsalar saboda suna duba bangaren Afirka ta Tsakiya inda 'yan tawaye suke fitowa suna shiga Kamaru. Ana kamasu kuma ana samun makamai a hannunsu.
A harin na garin Koncha an kashe 'yan Najeriya guda ukku da na Kamaru guda biyu dukansu suna cikin tawagar Majalisar Dinkin Duniar ce kuma su ne suke agazawa majalisar.
Ga rahoton Awal Garba da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5