Kasar Kamaru ta ci gasar cin kofin Nahiyar Afirka na yan kasa da Shekaru Sha Bakawai a bana, 2019, wadda aka kammala a kasar Tanzaniya.
Kamaru ta samu nasarar lashe kofin a karo na biyu ne bayan da ta doke takwararta ta kasar Guinea da ci 5 da 3 a bugun daga kai sai Maitsaron gida, bayan da su ka tashi canjaras, 0-0, wasan da aka yi shi ranar Lahadi da ta gabata a filin wasa na Dar-es-Salaam mai daukar mutane dubu 60.
Kasashe takwas ne suka fafata a wasan bisa tsarin rukuni biyu, wadda suka hada da Kamaru Guinea, Angola, da kuma Najeriya, inda wadannan kasashe hudu su ka yi nasarar samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya na 'yan kasa da shekaru 17, wadda kasar Brazil za ta karbi bakunci a bana.
Sauran kasashe hudu da suka buga kuwa sun hada da masu masaukin baki, kasashen Tanzaniya da Morocco, Senegal da Uganda; kuma wannan gasar karo na 13 kenan.
Bayan kammala gasar dan wasan kasar Angola mai suna Capita, shine ya zama dan wasa da ya fi zurara kwallo a gasar, inda ya ci kwallaye 4. Sai dan wasan Najeriya Wisdom Ubani da ya zo matsayi na biyu da kwallaye 3; Stève
Mvoué na Kamaru shi ne dan wasan da yafi kowa kokari a gasar da aka zaba. Kasar Angola ita ce ta zama kasa mai kungiya mafi da'a wato (Fair Play award).
Jimillar Kwallaye 36 aka jefa a cikin wasanni 16 da aka buga a gasar ta yan kasa da shekaru 17 na Afirka.