Makarantu da Jami’o’i a kasar Kamaru sun koma karatu a yau Litinin, duk kuwa da cewar adadin masu kamuwa da cutar coronvirus na kara hauhawa.
Ya zuwa yanzu kasar ta Kamaru na da mutum 6,380 da ke dauke da cutar, inda mutum 273 suka mutu. Amma hukumomin sun ce, adadin wadanda suke warkewa da irin matakan da aka dauka a makarantu ya ba su kwarin gwiwar cewar zasu iya magance yaduwar cutar.
Lokacin da ya ke Magana ta gidan talabijin na kasar a jiya Lahadi, Firai ministan kasar Joseph Dion Ngute ya ce, shugaban kasar Paul Biya ya umurci makarantu da ya rufe a ranar 17 ga watan Maris a matakin dakile yaduwar cutar, da su bude a yau 1 ga watan Yuni, domin kuwa mutum 3,630 cikin 6,380 fiye da kashi 19 cikin dari sun warke daga annobar mai kisa, ya kara da cewar matakan da aka samar don kare ‘yan kasar suna aiki matuka.
Firai ministan ya kara da cewar mafi yawa daga cikin mutum 2,300 da ke dauke da cutar suna samun sauki, kuma an dauki isassun matakai na rage hatsarin kamuwa da cutar a makarantu.