Kamaru Ta Bayyana ‘Yan Wasanta Da Zasu Kara Da Najeriya

BRAZIL-WORLDCUP/

Koch din Kamaru Volker Finke, ya bayyana tawagar ‘yan wasansa gabannin wasan kawance na ranar 11 gawatan Oktaba da Super Eagles.

Baki ‘daya kasashen zasu yi amfani damar wannan wasan amatsayin wani shiri ga wasannin nema shiga gasar cin kofin duniya mai zuwa na shekara ta 2018.

Kungiyar ta kamaru wadda akafi sani da Les Lion, zasu buga wasa da Samaliya ko Nijar, a ‘daya bangaren kuma Najeriya zata buga da Djibouti ko Switzerland.

Finke dai ya gayyato kwararrun ‘yan wasan da suka hada da Nicolas Nkoulou da Aurelien Chedjou, sai kuma ‘dan wasan baya Joel Matip da ‘dan wasan tsakiya Duo Eyong Enoh da Stephane M’bia, sauran ‘yan wasan kuma sun hada da Clinton N’Jie da Benjamin Moukandjo, sai kuma kwararren ‘dan wasan gaba Vincent Aboubakar.

‘dan wasan baya na kungiyar Dinamo Bucarest, Collin Fai da ‘dan wasan KV Ostende, Sebastien Siani sun sami kiran su na farko zuwa su bugawa kasar su wasa.