Kakakin gwamnatin kasar Issa Tchiroma Bakary shi ya bayyanawa manema labarai cewa dakarun kasar na musamman sun yi taho mu gama da 'yan Boko Haram inda suka kashesu da dama.
Gumurzun ya faru ne lokacin da dakarun Kamaru suka kai farmaki a mabuyan 'yan Boko Haram din biyo bayan cikakken bayani da suka samu daga 'yan kasa..
A farmakin sojojin Kamaru na musamman sun hallaka mayakan Boko Haram har 162 kana sojojin sun tarwatsa wuraren da 'yan ta'adan ke kera makamai. Haka kuma sojojin sun kama wasu daga cikin 'yan ta'adan.
Wasu kayan da sojojin suka sau sun hada da albarusai masu dama da rigunan garkuwa na yaki da bindigogi wadanda yanzu haka suna yin binciken kwakwaf a kai. Suna su san yadda aka yi 'yan Boko Haram suka sami kayan.
Mayakan Kamaru din sun kuma kwato daruruwan mutane daga hannun 'yan Boko Haram tare da kwato wasu mutane bakwai 'yan gida guda. Sun mayar dasu garuruwansu.
A yakin Kamaru ta rasa manyan kwamandojinta guda biyu masu shekaru 31 da haihuwa.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5