Kamaru Na Zaben Kananan Hukumomi, ‘Yan Majalisa

Malaman zabe suna shirya akwatunan jefa kuri'a a Yaounde, Kamaru

A yau Kamaru ta gudanar da zaben kananan hukumomi da na ‘yan majalisa a kasar.

Bayanai sun yi nuni da cewa, an yi zaben cikin lumana a yankunan da ke amfani da harshen Faransanci.

Sai dai an ga jinkiri a yankin bangaren da ke amfani da harshen Ingilishi, inda mayakan ‘yan aware suka gargadi mazauna yankin da kada su fita kada kuri’a.

Daruruwan masu kada kuri’a sun yi dogon layi a rumfunan zabe a makarantar Firaimare ta Bilingual Bastos mallakar gwamnati, a Yaounde, babban birnin kasar ta Kamaru.

Daga cikin wadanda suka yi zabensu da wuri-wuri, akwai Shugaba Paul Biya, wanda bayan da ya kada kuri’arsa, ya yi kira ga mutane da su fito kwansu da kwarkwatarsu su yi zabe.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su yi watsi da mutanen da ya kira “masu dauke hankalin jama’a” daga muhimman batutuwa.

A ‘yan shekarun bayan nan, kasar ta Kamaru tana ta fama da matsalar yunkurin bangarewar masu amfani da harshen Ingilishi, lamarin da har ya kai ga kai hare-hare.

Dubban mutane sun mutu sanadiyyar wannan rikici kana wasu miliyoyi sun fice a gidajensu.

Gabanin zaben, ‘yan awaren, sun sha alwashin hana ruwa gudu, amma shugaba Biya ya ce a zuba a gani.