Kusan mutane 2,000 'yan Najeriya, wadanda suke zaman gudun hijira a kamaru, hukumomin kasar suka tusa keyarsu dawowa cikin Najeriya ba tare da sun shirya ba.
Wannan mataki da kasar ta dauka ba zai rasa nasaba ba da hare haren ta'addanci na baya bayan nan da aka kai kasar a Marwa, inda mutane masu yawa suka halaka.
Kazalika, korar 'yan gudun hijirar yana zuwa ne 'yan kwanaki bayan ziyarar aiki da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai kasar.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya a jihar Adamawa, Alhaji Sa'adu Bello, yace sun koka ga hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD a Najeriya, inda suka nemi ta tuntubi reshenta dake kamaru, domin gaya musu yadda kamaru take tilastawa 'yan gudun hijirar barin kasar ba tare da wani shiri ba.
Sa'adu yace, akwai bukatar Kamaru ta shaidawa hukumar idan tana shirin korar 'yan gudun hijirar, sabo da, walau hukumar ta je ta dauko su, ko kuma kamaru ta kore su cikin mutunci.
Galibin wadanda aka koran suna dawowa Najeriya ne ta kan iyakar kamaru da ta Mubi, inda hukumar Red Cross da hukumar shige da fice suke karbar bakin hauren.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5