Batun karfafa gwaiwar kananan sana’o’I da matsakaitan masana’antu ta hanyar samar da kudin da zasu rinka tafiyar da ayyukansu yadda ya kamata na cikin manyan muradun cigaba mai dorewa guda 17 da kasashen duniya suka rattabawa hannu shekaru 8 da suka gabata.
Duk da cewa Najeriya na cikin jerin wadannan kasashe, har yanzu ma’abota kanana da matsakaitan masana’antu musamman a yankin arewacin kasar na ci gaba da nuna damuwa kan rashin samun tallafi ko lamunin bunkasa sana’o’in su.
La’akari da wadannan matsaloli ya sa masu ruwa da tsaki suka gudanar da taro na musamman a Kano domin lalubo mafita. Inda aka cimma kudurori da dama tsakanin bankuna da cibiyoyin tallafin kudade domin bunkasa sana’o;i.
Shi kuma alhjai Babangida Lamido, wani mai sharhi akan bunkasa harkokin kananan sana’o’I da matsakaitan masana’antu yace taron ya zo akan gaba duk da cewa akwai sauran rina a kaba.
Ya ce, an tattauna mahimman al’amura kana yayi fatar Allah ya tabbatar da alkhairi, sai dai kumma ya nuna rashin jin dadi, la’akari da cewa babu wani wakilin gwamnati ko da mutum daya sannan dole sai gwamnati ta bada goyon bayan sannan ya yiwu. Ya kuma kara da cewa, kudi da har idan aka yi nasara mutane suka samu, zai taimaka musu matuka.
A nasa bangaren Farfesa Murtala Sani Sagagi na jam’iar Bayero a Kanon Dabon Najeriya, ya ce Dole ne sai anyiwa su kansu bankunan takara domin basa son baiwa masu kananan ‘yan kasuwa bashi. Sabo da haka sun fi son mutanen da zasu basu bashin biliyoyi, sannan kudin ruwan da ake dorawa akan basusukan yayi yawan da ‘yan kasuwan ba za su iya tunkarar bankunan ba. Sannan kuma, dole sai an zauna an hada kan wadannan ‘yan kasuwa an illimantar da su kuma an zaburar da su akan hanyoyin kasuwanci na zamani da kuma hanyoyi da zasu bi domin su kai ga samun wannan kudin.
Hakan na kara nuna bukatar da ke akwai ga gwamnatocin arewacin Najeriya su mai da hankali akan kanana da matsakaitan sana’o’I domin ceto yankin arewa daga barazanar durkushewar tattalin arziki.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5