Shekaru hamsin da bakwai da samun ‘yancin kan Najeriya, amma manazarta na ganin har yanzu kasar ta kasa shawo kan matsallar rarrabuwan kai dake addabar ‘yan kasar duk da yunkurin da gwamnatoci suka sha yi tun daga samun ‘yancin har zuwa karshen yakin bazaza har kawo yanzu domin tabbatar da hadin kan ‘yan kasar ana ci gaba da samun rarrabuwan kawona masamman ta bangaren addini da kabilanci da kuma bangaranci.
Wannan lamarin a cewar wani Malami a jami’ar Uthman Danfodio dake Sokoto, Farfesa Bello Bada, baya rasa nasaba da irin yanayi kasar Najeriya da kuma mutanentayana mai cewa tafiya ta kasance da wuya kwarai da gaske saboda Najeriya ta kasance kasa mai yawan mutane kuma da lardodi daban daban da kabilu daban daban da Sarakunan su.
A lokacin da aka ce za a yi tafiya daya tarbiyar ta kasance daban daban wasu kuma a cibiyar kasuwanci kasar suke tilas wannan abin ya anfane su, idan akayi irin wannan hadin ganbiza tafiyar tana da wuya kwarai shi yasa aka samu juyin mulki da aka samu na farko kuma wannan juyin mulki ya kawo ana tuhumar juna tsakanin manyan kabilun Najeriya, domin juyi mulkin yazo da kashe kashen shugabani.\Shekaru dari da uku (103) kenen da aka hade bangarorin Najeriya a matsayin kasa daya dungulalliya.
Amma masu lura da al’amuran yau da kullum na ganin kalubalan hadin kai na shafan matakin cigaban kasar yanzu idan aka kwatanta da sauran kasace irinta a duniya.
Your browser doesn’t support HTML5