KALLABI: Na Dauki Nawayar Gidan Aurena Na Tsawon Shekaru 25-Fatumatu Dangana, Afrilu,09, 2023

Shirin Kallabi

Abinda ya dauki hankalin shirin a wannan makon shine fadi tashin da mata ke yi a gidan aure da ba safai a ke yin magana a kai ba, kuma sau da dama, matan da ke ta-maza su ga sun rufawa gidajen aurensu asiri, ba a san suna yi ba balle a yaba masu.

Wannan makon shirin ya yi hira da Fatumatu Mohammed Watara, wata mace a kasar Ghana da ta sami kanta a cikin irin wannan hali tun daga tashinta har a gidan aurenta.

Saurari shirin domin karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

KALLABI: Hira da Fatumatu Mohammed Watara, 09, 2023