Kalaman Shugaba Buhari Na Kara Ta'azzara 'Yan Adawa

Yanzu haka dai a Najeriya, tun bayan da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bayyana cewa wa'adin mulkinsa a karo na biyu zai kasance mai tsauri, 'yan kasar da masana ke bayyana ra'ayoyinsu mabanbanta.

Kawo yanzu ma wasujama'ar kasar suna kallon kalaman nasa a matsayin kalamai masu tayar da hankali, yayin da a bangare guda wasu kuma suka fahimci inda ya dosa da ma'anar kalaman daidai da tunani ko kuma ra'ayin shugaban a kan abinda yake nufi.

Hon Abdullahi Adamu, masanin tattalin arziki, kuma sakataren jam'iyar PDP a jihar Adamawa, ya bayyana yadda suke kallon kalaman na shugaban kasa Buhari.

Cikin kwanakin nan dai shugaban Najeriya, yi wasu kalaman da kan jawo martani da kuma cece-kuce.

Wai me shugaba Buhari ke nufi da wadannan kalaman nasa? Mr Boss Mustapha sakataren gwamnatin tarayya shi ya jagoranci tawagar 'yan majalisar zartaswa, a lokacin yiwa shugaban kasa murna Inda shugaban yayi wannan bayani.

Ga rahoton wakilin shashen Hausa na Muryar Amurka Ibrahim Abdul’Aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Kalaman Shugaba Buhari Na Kara Ta'azzara 'Yan Adawa 2'20"