Ga dukan alamu jawabin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi a wurin taron kungiyar hadin kan Afirka da ake kira AU a takaice, wanda aka yi a kasar Habasha, inda ya ce gwamnatinsa zata tabbatar an sako duk wani dan Najeriya da ke hannun 'yan kungiyar Boko Haram kamar yadda aka ceto wasu daga cikin ‘yan matan makarantar Chibok, ya kawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan kasar.
Wasu 'yan Najeriya na jefa alamar tambaya akan ko shugaba Buhari zai iya kawo karshen ta'addancin 'yan Boko Haram a cikin shekaru uku da suka rage masa a mulki ko a'a, duba da cewa ya gaza yin hakan a shekaru biyar da suka wuce.
Daya daga cikin shugabannin gamayar kungiyoyin matasan Arewacin Najeriya, Ashir Sheriff, ya ce shugaba Buhari, daga ayyuka zuwa tsarin sa, ba su nuna alamun cewa zai cimma wannan burin akan matsalar tsaro a Najeriya.
Sannan ya kara da cewa jama'a da wasu shugabanni a kasar sun yi kira da a canza wasu manyan jami'an tsaro a kasar, amma shugaba Buhari ya yi burus. Talakawa na kuka, ga rashin aikin yi, rashin abinci da musamman rashin tsaro, duk da haka babu wani abin da aka canza, a cewar Sheriff.
A saurari cikakken rahoto cikin sauti daga Abuja.
Your browser doesn’t support HTML5