Bayanan na Dr.Gadon Kaya sun jawo martani tsakanin masu kushewa da masu cewa biri ya yi kama da mutum.
Wannan kalami bai yi wa jami’an kiwon lafiya dadi ba, don har an samu barazanar kai kara kotu don bin kadun abun da su ke cewa sam malamin bai yi mu su adalci ba.
A sharhin sa kan lamarin Sheikh Musa Yusuf ya ce akwai bambanci tsakanin ba da shaidar tabbatar abu ko akasin haka a gaban kotu da kuma gaskiyar abu na faruwa ko kuwa a’a.
Asadus sunnah ya ba da labarin abun takaici da ya same shi a wani asibiti da ta kai ga matar sa mai nakuda ta galabaita har ta kai ga bayan sun tafi wani asibiti a ka zaro yaro babu rai.
Malamin ya kawo misalai na wadanda su ka fusakanci cin zarafi a sanadiyyar irin wannan aiki, don haka ya ke ganin matakan gyara kayan ka ya dace a dauka ba maida martanin kare abokan aiki ba