Kalaman Donald Trump Sun Haifar Da Rashi Jituwa A Jam'iyyar Republican

Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jamiyyar Republican Donald Trump wanda ya kwashe sati guda yana cece kuce akan batun Khizr da Ghazala Khan, iyayen wani sojan Amurka da aka kashe a Iraqi, ya janyo wasu ‘yan jamiyyar tasu ta Republican fitowa fili suna sukar dan takarar nasu.

Wanan lamari dai ya kara fito da irin rashin jittuwar da ake samuwa tsakanin dan takarar da wasu manyar jamiyyar tasu.

Meg Whitman, wata fitattar shugabar kanfanin kere-kere da ta nemi zamowa gwamnan jihar Califonia a cikin shekarar 2010 amma bata samu ba, ta fada wa jaridar The New York Times a yammacin jiya talata cewa zata goyi bayan yar takarar jamiyyar Democrat Hillary Clinton kuma zata nema mata gudun muwar kudi Kana ta kira Donald Trump mara gaskiya.

Haka shima dan majilisar wakilan Amurka Richard Hanna na New York shine zababben dan majilisar farko a halin yanzu da ya fito fili ya nuna goyon bayan sa ga Clinton, yace yayi tir da kalaman dan takarar jamiyyar su ta Republican game da Khan.

Wannan nuna goyon bayan wadannan mutanen yazo ne yan sa’oi bayan da shugaba Obama ya dauki matakin nisanta shugaban Amurka da kalaman dan takarar shugabancin kasa.Lokacin ne shugaba Obama yace Trump bai cancaci zama babban kwamandar askarawar Amurka ba.