Yayin da yake jawabi wajen raba kayan rage radadin fatara da wata 'yar majalisar wakilan tarayya Binta Bello ta samarma al'ummarta a Kaltungo, Aminu Waziri Tambuwal kakakin majalisar wakilan Najeriya ya kira 'yan Najeriya da su cigaba da zaman lafiya.
WASHINGTON, DC —
A cikin jawabin da yayi a Kaltungo wurin kaddamar da kayan rage radadin fatara da 'yar majalisar wakilai Binta Bello ta tanadawa al'ummarta, Aminu Waziri Tambuwal ya gargadi 'yan Najeriya su zauna lafiya da juna.
Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya jaddada mahimamancin zaman lafiya abun da ya ce shi kadai zai sa Najeriya ta cigaba da kuma cin moriyar mulkin dimokradiya. Idan babu zaman lafiya da kyar a iya yin komi na cigaba. Wajibi ne jama'a su hada kai su tabbatar da zaman lafiya tsakaninsu. A gujewa nuna banbanci ko na kabilanci ko na addini.
A zabi shugabanni masu adalci a kuma bisu. Shugabanci bashi tafiya idan babu adalci. Domin haka a zabi mutane masu adalci da son jama'arsu ko Musulmai ne ko Kirista ne domin a samu cigaba.
A nashi jawabin gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo ya kalubalanci sauran da suke rike da mukamai ne. Yace Binta Bello tayi abun yabo. Yakamata 'yan majalisun tarayya dake wakiltar jihar da 'yan majalisar dokokin jihar da kwamishanoni da duk masu rike da mukami su yi koyi da abun da Binta tayi.
Ga rahoton Sa'adatu Fawu.

Your browser doesn’t support HTML5