Kakakin karamar majalisar dokoki ta Masar yana shirin kiran zaman majalisar a yau talata, zai kuma yi ko oho da umurnin majalisar kolin soja da hukumcin kotun kolin kasar.
Wannan mataki nasa ya biyo bayan takardar umurnin da shugaba Mohammed Morsi ya bayar ta maido da majalisar dokokin a bayan da shugabannin sojoji suka rushe ta a watan jiya saboda magudin zabe.
Kotun koli ta bayyana cikakken goyon baya ga matakin da sojojin suka dauka, sannan ta sake jaddadawa a jiya litinin cewa hukumcinta shi ne na karshe kuma na dole. A yau talata ana sa ran kotun zata yanke hukumce-hukumce da dama a game da daukaka karar da aka yi kan takardar umurnin da shugaban ya bayar.
Magoya bayan Mr. Morsi sun yi kiran da a gudanar da gangamin mutane miliyan daya yau talata a birnin al-Qahira domin bayyana goyon baya ga matakin da ya dauka.